Zanga-zangar Iraqi ta tilasta rufe Ma'aikatu da Makarantu

Masu zanga-zanga adawa da gwamnati a Iraqi sun tilasta rufe makarantu da ma'aikatu
Masu zanga-zanga adawa da gwamnati a Iraqi sun tilasta rufe makarantu da ma'aikatu REUTERS/Khalid al-Mousily

MASU Zanga zanga a kasar Iraqi sun mamaye titunan birnin Bagadaza, inda suka rufe tituna abinda ya hana dalibai zuwa makarantu da kuma hana ma’aikata zuwa ofisoshin su.

Talla

Masu zanga zangar dake bayyana damuwa kan cin hanci da rashawa da kuma rashin ayyukan yi, sun bijirewa duk wani tayi na janyewa da kuma tirsasawar jami’an tsaro.

Rahotanni sun ce bayan Bagadaza, an gudanar da zanga zangar a birnin Diwaniyah.

A ranar daya ga watan Oktoba aka fara wannan zanga – zangar nuna rashin amincewa da rashawa da rashin aikin yi da suka yi wa Iraqi dabaibayi, amma hukumomi suka yi wa masu zanga – zangar diran mikiya, har da dama daga cikin suka mutu.

Tun da aka fara wannan zanga – zangar, sai dada habaka take yi, biyo bayan goyon baya daga dalibai da kungiyoyin ‘yan kasuwa, wadanda suka ba da sanarwar gangamin neman sauyi ba tare da tarzoma ba.

A birnin Bagadaza, daliban jami’a ne suka yi amfani da motoci wajen datse hanyoyn da suka hada unguwanni a ranar Litinin din nan, yayin da ‘yan sanda suka zura musu ido.

A birnin Diwaniyah da ke kudancin kasar, wani kyalle ne rataye a mashigin shelkwatar lardi dauke da rubutun da ke cewa, “ Al’umma ta yi umurnin a rufe”.

Makarantu daofisoshin gwamnati na rufe a birnin Bagadaza, da sauran Birane da dama a kudancin kasar.

Haka ma a birnin Basramai arzikin danyen man fetur, an rufe makarantun gwamnati a karon farko tun daaka fara wannan zanga – zangar a Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.