Iran ta koma aikin inganta nukiliya

Shugaban Iran Hassan Rouhani.
Shugaban Iran Hassan Rouhani. © REUTERS/Brendan Mcdermid

Hukumar kula da makamashin atom ta Iran ta ce kasar ta koma ci gaba da tacewa tare da inganta makamashin nukiliya a tashar karkashin kasa ta Fordow da ke kudancin birnin Tehran.

Talla

A Alhamis din nan Iran ta fara zuba wasu sinadari daga makamashin uranium cikin na’urori, a wani mataki na kaucewa daga yarjejeniyar dakile aikin ta na inganta makamashin uranium ta 2015 da ta sha alwashin sabawa.

Shi dai daukar matakin da Iran ta yi, ya sake tada wata sabuwar damuwa ga kasashen da ke cikin yarjejeniyar nukliyar ta duniya da aka cimma a 2015 a Vienna.

A karkashin yarjejeniyar dai mahukuntan Tehran sun amince su rage kaifin inganta sanadarin makamashin nukliyar da kasar ke yi, domin samar da tabbacin dake nuna cewa aikin nukliyar na farar hula ne, ba na soja ba, a yayin da ita kuma za ta amfana da cire mata takunkuman kariyar tattalin arzikin da kasashen duniya suka kakaba mata, da ya takaita ci gaban tattalin arzikinta

Jamhuriyar musulunci ta Iran dai a ranar Talata da ta gabata ne ta bayyana aniyarta na sake komawa aikin inganta ma’adanin na uranium, har ma ta kai ga rufe cibiyar ta Fordo dake da tazarar km 180 kudancin Téhéran) dungurumgum, kamar yadda yarjejeniyar ta Vienne ta tanada

Iran ta dau wannan mataki ne kwana guda bayan cikar wa’adin da ta baiwa kasashen dake cikin yarjejeniya da suka hada (China, France, Igland, Russie da jamus) na su taimaka mata ta samu ta haye takunkuman da Amurka ta mayar a kan ta bayan ficewar ta daga cikin yarjejeniyar a 2018, taimakon da kasashen na turai suka kasa yi mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI