Isra'ila

Isra'ila ta kashe babban kwamandan Falasdinawa

Dakarun Isra'ila sun halaka babban kwamandan mayakan Falasdinawa ta Islamic Jihad.
Dakarun Isra'ila sun halaka babban kwamandan mayakan Falasdinawa ta Islamic Jihad. AFP/BASHAR TALEB

Sojin Isra’ila sun kashe babban kwamandan mayakan kungiyar Falasdinawa ta “Islamic Jihad” na yankin Gaza.

Talla

Tuni dai mayakan Falasdinawan suka maida martani da makaman roka, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar sabon yaki tsakanin bangarorin biyu.

Jim kadan bayan sanar da kai farmakin ne, kungiyar ta Islamic Jihad ta tabbatar da mutuwar babban kwamandan nata a Gaza Baha Abu Al-Ata mai shekaru 42, tare da mai dakinsa a gidansu da jiragen yakin Isra’ilar suka ragargaza, gami da halaka wasu mutanen 3 da jikkata 18.

Farmakin Isra’ilar ya jawo zazzafan martani daga Falasdinawan, inda mayakan na Islamic Jihad suka harba makaman roka kimanin 50 kan wasu yankunan Isra’ilar ciki har da biranen Kudus da Tel Aviv, sai dai rundunar sojin kasar ta ce ta yi nasarar kakkabo 20 daga cikin makaman, amma duk da haka mutane 29 suka jikkata.

Isra’ila na zargin Abu Al-Ata da jagorantar hare-haren makaman rokar da aka kai mata daga zirin gaza, da kuma shirya kai mata wasu munanan hare-haren nan da ‘yan kwanaki.

Islamic Jihad ita ce kungiyar mayakan Falasdinawa ta 2 mafi karfi a yankin Gaza bayan Hamas, wadda suka kulla yarjejeniyar kawance.

Yanzu haka dai Isra’ila ta girke dakarunta a kan iyakar yankin Gaza cikin shirin kaddamar da yaki ko kariya daga barzanar hare-haren mayakan Falasdinawan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.