Myanmar-Rohingya

ICC ta amince da rahoton binciken zargin kisan musulmi kan mahukumtan Myanmar

Aung san suu kyi ta damu da halin da kisan da ake yiwa kabilar Rohingyas
Aung san suu kyi ta damu da halin da kisan da ake yiwa kabilar Rohingyas Dr Meddy

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta amince da rahoton binciken da aka shafe tsawon lokaci ana yi, kan jagorar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi a gabanta, saboda zargin da ake mata da hannu wajen azabtar da Musulmi Yan kabilar Rohingya.

Talla

Sanarwar da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta fitar, na cewa ta umarci mai gabatar da kara ya cigaba da gudanar da bincike karkashin tsarin hukuncin kotun, a kan laifukan da jagorar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi ta aikata a kan Musulmi Yan kabilar Rohingya.

Sanarwar ta ce binciken zai duba zarge zargen da ake yi wa suu kyi, na samunta da hannu kan shiryayyen laifi na cin zarafin dan adam, tilasta maida yan gudun hijirar rohingya gida a matsayin laifin take hakkin dan adam, tare da yankewa yan kabilar rohingya hukunci na rashin adalci saboda banbancin addini ko kabila

Kotun ICC ta ce a yau alhamis ta umarci wasu jerin alkalanta su soma bin diddigi wajen gudanar da bincike kan duk wani abu mai kama da laifi da aka yi wa musulmi yan kabilar rohingya.

Myanmar ta kaddamar da harin soji a shekarar 2017 wanda ya tilastawa musulmi yan kabilar rohingya dubu 740 tserewa zuwa sansanonin kasar ta Bangladesh, lamarin da majalisar dinkin duniya ta ayyana a matsayin kisan kare dangi .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.