Iran

Mutum 1 ya mutu a zanga-zangar da ta barke a Iran

Karin farashin man fetur ya haddasa zanga-zanga a sassan Iran.
Karin farashin man fetur ya haddasa zanga-zanga a sassan Iran. Nazanin Tabatabaee/WANA/Reuters

Akalla mutun daya ya gamu da ajalinsa yayin da wasu suka jikkata a zanga-zangar da ta barke a sassan kasar Iran Asabar din nan, kwana guda bayan da gwamnatin kasar ta sanar da daukar matakin kara farashin man fetur.

Talla

Rahotanni sun ce zanga-zangar tafi muni a birnin Sirjan dake yankin tsakiyar kasar, inda a daren jiya, daruruwan jama’a suka yi yunkurin kona wani rumbun adana man fetur, amma yan sanda suka watsa su.

Gwamnatin ta Iran sanar da karin faranshin man fetur din ne da akalla kashi 50, matakin da ta ce zai taimakawa kasar samun karin kudaden shigar da adadinsu ya kai dala biliyan 2 da miliyan 55 a shekara, kwatankwacin kudin kasar Rial triliyan 300.

Karin farashin man fetur din da gwamnatin Iran ta yi ya zo ne a dai dai lokacin da aka gano wani katafaren filin dauke da arzikin man fetur din da yawansa aka kiyasta ya kai ganga biliyan 53 a yankin kudu maso yammacin kasar.

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce filin dake lardin Khuzestan, zai karfafa rumbun man kasar da akalla kashi 1 bisa 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI