Isa ga babban shafi
Sri Lanka

Gotabaya ya lashen zaben Sri Lanka

Gotabhaya Rajapaksa dan siyasar da ya lashen zaben Shugaban kasar Sri Lanka
Gotabhaya Rajapaksa dan siyasar da ya lashen zaben Shugaban kasar Sri Lanka REUTERS/Dinuka Liyanawatte
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 1

Gotabaya Rajapaksa da ya jagoranci murkushe mayakan Tamil Tigers a Sri Lanka ya lashe zaben shugaban kasar da akayi a karshen mako, inda yayi alkawarin zama shugaban daukacin al’ummar kasar.

Talla

A yau lahadi ne hukumar zaben kasar ta fitar da sakamakon zaben.

Hukumar zaben kasar tace Rajapaksa ya samu sama da kashi 52 na kuri’un da aka kada, yayin da abokin takarar sa kuma dan takaran Jam’iyya mai mulki, Sajith Premadasa ya samu kusan kashi 42.

Tuni Premadasa ya amsa shan kaye, kuma ya taya Rajapaksa murnar nasarar da ya samu.

Ranar litini gobe kenan ake sa ran sabon Shugaban kasar zai sabi rantsuwar kama aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.