Iran

Jami'an tsaron Iran sun kame mutane 40

Jami'an tsaron Iran yayin kokarin watsa dandazon masu zanga-zanga a babban titin da ya ratsa birnin Tehran. 16/11/2019.
Jami'an tsaron Iran yayin kokarin watsa dandazon masu zanga-zanga a babban titin da ya ratsa birnin Tehran. 16/11/2019. ©Nazanin Tabatabaee/WANA (West Asia News Agency) via REUTERS

Masu zanga-zangar adawa da karin farashin man fetur a Iran sun yi arrangama da jami’an tsaro a birnin Yazd dake tsakiyar kasar, abinda ya kai ga kame mutane 40.

Talla

Babban lauyan gwamnati a yankin na Yazd Mohammed Hadadzadeh ya ce an kame mutanen ne, saboda barnar da suka tafka ta lalata tarin dukiya yayin zanga-zangar.

Kamen na zuwa ne, jim kadan bayan da gwamnatin Iran ta gargadi masu zanga-zanga a sassan kasar kan haddasa tashin hankali, inda tace a shirya take ta baiwa jami’an tsaro damar yin amfani da karfi wajen murkushe su.

A ranar asabar zanga-zanga ta barke a sassan Iran kwana guda bayan da gwamnatin kasar ta sanar da kara farashin man fetur da akalla kashi 50 cikin 100, matakin da ta ce zai taimakawa kasar samun karin kudaden shigar da adadinsu ya kai dala biliyan 2 da miliyan 55 a shekara, kwatankwacin kudin kasar Rial triliyan 300.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI