Iran: Masu bore sun kashe jami'an tsaro

Wani gidan mai da masu zanga-zanga suka kone a yankin Eslamshahr, dake gaf da birnin Teheran.
Wani gidan mai da masu zanga-zanga suka kone a yankin Eslamshahr, dake gaf da birnin Teheran. AFP

Masu bore a Iran sun kashe jami’an tsaron kasar 3 ta hanyar daba musu wuka a yammacin birnin Teheren.

Talla

Zuwa yanzu mutane 5 aka tabbatar da mutuwarsu yayin zanga-zangar da ta barke a wasu biranen kasar ta Iran a ranar Juma’a, bayan da gwamnati ta sanar da karin farashin man fetur da kashi 50 cikin 100, da.

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce karin farashin man fetur din zai taimakawa kasar samun karin kudaden shigar da adadinsu ya kai dala biliyan 2 da miliyan 55 a shekara, kwatankwacin kudin kasar Rial triliyan 300.

Matakin kara farashin man a Iran ya zo ne kwanaki kalilan bayan sanar da gano arzikin gangar danyen mai akalla biliyan 53 kwance a wani fili dake kudancin kasar.

Yazu haka dai Iran na kan fama da takunkuman karya tattalin arzikin da shugaba Donald Trump ya kakaba mata, bayan janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar da Iran din ta cimma da manyan kasashen Turai a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI