Isa ga babban shafi
Isra'ila

An gaza kafa sabuwar gwamnati a Isra'ila

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu Reuters
Zubin rubutu: Michael Kuduson
Minti 1

Da alama sai an sake gudanar da wani sabon zabe kafin kafa sabuwar gwamnati a Israila, ganin yadda Avidgor Libermann yaki baiwa Benny Gantz da Benjamin Netanyahu goyan bayan da suke bukata domin kafa gwamnati.

Talla

Netanyahu da Gantz sun gaza samun rinjaye kujerun Majalisun da ake bukata domin kafa gwamnati, bayan gudanar da zabe sau biyu.

Shugaban kasar Reuben Rivlin ya fara baiwa Netanyahu kwanaki 28 domin kafa gwamnati amma ya gaza samun goyan bayan da yake bukata, abinda ya sa aka baiwa Gantz kuma shima har zuwa wa’adin daren jiya bai samu nasara ba.

Hakan na nufin za a sakewani zaben a farkon shekarar 2020, babban zabe na uku kenan a tsakanin watanni 12.

Netanyahu, wandake fuskanta tuhume-tuhumen rashawa daya musanta,zai ci gaba da kasancewa a matsayin shugaban riko har sai an gudanar dazabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.