Hong Kong

China ta goyi bayan jagorar Hong Kong duk da shan kaye a zabe

Wasu matasa da ke murnar nasarar masu rajin kafa tsarin Dimokradiyya a yankin.
Wasu matasa da ke murnar nasarar masu rajin kafa tsarin Dimokradiyya a yankin. Reuters/Thomas Peter

Gwamnatin China ta nuna goyon baya ga jagorar yankin Hong Kong Carrie Lam bayan shan kayenta a zaben kananan hukumomi da ya gudana, zaben da bangaren masu rajin kafa tsarin Dimukradiyya suka lashe da gagarumin rinjaye.

Talla

A wani taron manema labarai da ma’aikatar harkokin wajen Hong Kong ta kira karkashin jagorancin Geng Shuang ta bayyana cewa gwamnati na da cikakken goyon baya daga China, duk da sakamakon zaben wanda ake gani a matsayin babbar koma baya ga

Rahotanni sun bayyana cewa masu rajin tabbatar da tsarin dimokradiyya a yankin sun lashe kujeru 263 yayinda jam'iyya mai mulki ke da kujeru 59.

Zaben wanda ke zuwa bayan zanga-zangar kin jinin gwamnati ta tsawon watanni, zai haifar da sakamako mai kyau ga masu rajin kafa tsarin dimokradiyya tare da karshen kutsen China a harkokin gudanarwar yankin.

Tuni dai Jagorar yankin na Hong Kong Carrie Lam ta ce a shirye take ta gana da jagororin masu rajin kafa tsarin na Dimokradiyya don lalubo bakin zaren, yayinda China ta nuna halin ko’inkula da nasarar ta bangaren adawa.

Tsawon watanni matasa da jagororin masu zanga-zanga na fafutukar ganin shugaba Carrie Lam mai ra'ayin China ta amince da samar da sauye-sauye a tsarin tafiyar da shugabancin yankin amma ta ki bayar da hadin kai.

Yanzu haka dai dubban matasa ne ke ci gaba da gangamin nuna farin ciki da nasarar tasu a zaben,ko da dai tuni China ta bayyana cewa babu abin da sakamakon zaben zai sauya a tsarin gudanarwar yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI