Iraq

Jami'an tsaron Iraqi sun murkushe masu zanga-zanga

Masu zanga-zangar sun kona ofishin jakadancin Iran kurmus
Masu zanga-zangar sun kona ofishin jakadancin Iran kurmus Hussein FALEH / AFP

Jami’an tsaron Iraqi sun murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 22, yayin da masu zanga-zangar suka cinna wuta a ofishin jakadancin Iran.

Talla

Masu zanga-zangar sun kona ofishin jakadancin Iran kurmus da ke birnin Najaf, inda suke ta ihun cewa, "Nasara ta Iraqi ce" tare da fadin "Iran ta yi wace", yayin da mahukuntan Tehran suka yi tur da wannan farmakin.

Firaministan Iraqi Adel Abdel Mahdi ya umarci hafsoshin kasar da su tare a yankunan lardunan da ke fama da rikici da zummar samar da tsaro da zaman lafiya.

Sai dai Firaministan ya kori Kwamandan sojin kasar bayan murkushewar da ta yi sanadinyar mutuwar mutane 22 a birnin Nasariyyah.

Jami’an tsaron sun yi amfani da karfin da ya wuce kima wajen fatattakar masu zanga-zangar da ke zaman dirshen a kan wasu gadoji biyu, inda suka harbe su da da bindiga, abin da ya yi sanadiyar ajalinsu wasunsu tare da jikkata kimanin 150.

Tuni dai aka kafa dokar takaita zirga-zirga a biranen Najaf da Nasariyyah sakamakon wannan tashin hankali.

Masu zanga-zangar na zargin Iran da bai wa gwamnatin Iraqi goyon baya a daidai lokacin da suke fafutukar hambarar da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.