Hong Kong

Zanga-zangar Hong Kong ta sauya salo

Masu zanga-zangar yankin Hong Kong.
Masu zanga-zangar yankin Hong Kong. REUTERS/Laurel Chor

Dubunnan matasa masu zanga-zangar neman sauyi a Hong Kong sun sake fita kan titunan yankin bayan hutun dan lokaci biyo bayan nasararsu a zaben shiyyoyi cikin makon jiya.

Talla

Tun daga tsakaddaren jiya ne zanga-zangar ta faro bayanda tawagar matasan suka kokarin balle shingayen binciken ‘yan sanda matakin da yak ai ga arangama tare da harba hayaki mai sanya hawaye karon farko tun bayan ranar 24 ga watan Nuwamba.

Yayin gangamin na yau matasan sun shirya kayataccen tattaki zuwa Ofishin jakadancin Amurka don mika godiya kan goyon bayan da suka samu yayin zaben dama goyon bayansu ga zanga-zangar dungurum.

Ka zalika tawagar matasan za ta gabatar da jawabin kai tsaye da zai nemi gudanar da zaben ‘yan Majalisu da jagorori a matakan jihohi da yankuna baya ga zartas da hukunci kan zargin cin zarafin masu zanga-zangar da ake kan jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI