Batagari sun sayar da matan Pakistan 600 ga 'yan China- bincike

Wasu iyaye a Pakistan da aka sace 'ya'yansu a ka sayar a China.
Wasu iyaye a Pakistan da aka sace 'ya'yansu a ka sayar a China. REUTERS/Mohsin Raza

Wani sabon bincike da mahukuntan Pakistan suka gudanar kan safarar bil’adama ya nuna yadda batagari suka sayar da ‘yan matan kasar fiye da 600 ga ‘yan China cikin wa’adin da bai gaza shekaru 2 ba.

Talla

Sabon rahoton hukumar da ke yaki da safarar bil’adama a kasar ta Pakistan ya nuna cewa anyi safarar mata galibi masu karamin karfi guda dari 6 da 29 cikin shekaru 2 da suka gabata zuwa China, adadin da ke matsayin mafi yawa da hukumar ta taba samu.

Wasu majiyoyin tsaro sun bayyana cewa, 'yan matan da aka yi nasarar cetosu sun ki amincewa su bayar da cikakken bayani kan yadda safarar ta su ta gudana sakamakon barazanar da suka fuskanta.

Sadiq Iqbal jami'in da ke fafutukar kare hakkin bil'adama ya bayyana cewa suna dukkanin kokarin wajen ganin sun dawo da ilahirin 'yan matan da aka sayar a Chinan ga iyayensu.

Babu cikakken adadin matan da aka yi nasarar cetowa yayin binciken na baya-bayan nan, sai dai Sadiq Iqbal ya bayyana cewa gwamnatin Firamnista Imran Khan ta shirya tsaf don magance matsalar.

Kasar Pakistan da makociyarta India na fama da kalubalen satar mata tare da sayar da su a ketare don yin karuwanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.