Hari kan masu zanga-zanga ya hallaka mutum 12 a Iraqi
Wallafawa ranar:
Akalla mutane 12 aka tabbatar da mutuwarsu yayinda wasu da dama kuma suka jikkata sanadiyyar farmakin da wasu mutane suka kaddamar kan dandazon masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Baghdad na Iraqi.
Harin dai na zuwa ne a dai dai lokacin da Amurka ta zargi Iran da rura wutar zanga-zangar Iraqi tare da sake lafta mata wasu manyan takunkuman karya tattalin arziki.
Tun cikin Oktoba ne matasa ke zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin ta Iraqi wadda suka bayyana ga kasasshiya bayanda ta rasa samar da ayyukan, a bangare guda kuma tsadar rayuwa ke kara tsananta baya ga yadda tattalin arzikin kasar ke ci gaba da durkushewa, zanga-zangar da ke samun cikakken goyon baya daga Iran.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu