India

Gobara a rukunin Masana'antu na India ta hallaka mutum 45

Akalla mutane 45 aka tabbatar da mutuwarsu kawo yanzu yayinda ake tsammanin karuwar adadin bayan wata gobara da ta tashi a rukunin masana’antu can a birnin New Delhi na India.

Wani bangare da ya kama da wuta.
Wani bangare da ya kama da wuta. REUTERS
Talla

Gobarar wadda ta tashi da asubahin yau Lahadi ta bakin majiyar jami’an tsaro ta kone kaso mai yawa na masana’antun da ke yankin baya ga dakunan ajiye kayaryaki.

A cewar Sunil Chaoudary shugaban hukumar kashe gobara ta birnin New Delhi sun yi nasarar tseratar da mutane 50 ko da dai akwai wasu da suka bace kuma ake tsammanin suna makale a cikin gine-ginen.

Kawo yanzu dai ana ci gaba da aikin kashe gobarar wadda ba a kai ga gano musabbabinta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI