Myanmar-Rohingya

Aung San Suu Kyi ta gurfana gaban ICC kan kisan 'yan Rohingya

Shugabar Gwamnatin Myanmar da tawagarta lokacin da suke isa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.
Shugabar Gwamnatin Myanmar da tawagarta lokacin da suke isa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya. 路透社

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC da ke birnin Hague a Holland za ta fara sauraren zargin da ake yi wa mahukuntan kasar Myanmar da aikata kisan kare dangi kan musulmi 'yan kabilar Rohingya da ke matsayin tsiraru a kasar ta Mynmar.

Talla

Shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi da kanta ce ta ke kokarin kare kasar a game da wannan tuhuma wadda kasar Gambia ta shigar da karan amadadin al’ummar ta Rohingya bisa zargin cewa Myanmar ta karya yarjejeniyar kasa da kasa da aka amince da ita a shekarar 1948 da ta hukunta wanda ya aikata kisan kare dangi.

Gambia dai na zargin gwamnatin Myanmar da hannu wajen kisan kare dangin da aka yiwa tsirarun musulmin ‘yan kabilar Rohingya a wani yunkuri na shafe kabilar.

Cikin shekarar 2017 ne rikici ya tsananta a jihar Rakhine yankin da ‘yan Kabilar ta Rohingya su ke cikin kasar ta Myanmar inda Soji suka rika yiwa tsirarun musulmin kisan kiyashi baya ga fyade ga matayensu da kuma jefa mazajensu a gidajen yari.

A wancan lokaci dai kusan mutum miliyan guda daga ‘yan kabilar ta Rohingya ne suka tsere daga kasar inda kimanin dubu dari 740 ke gudun hijira a Bangladesh.

Guda cikin jagororin ‘yan kabilar ta Rohingya a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Bangladesh Sayed Ulla ya ce Suu Kyi ba ta da wata hujja da za ta kare kanta.

‘Yan gudun hijirar ta Rohingya dai na da ra’ayin cewa Suu Kyi na cikakkiyar masaniya baya ga nuna goyon baya ga cin zarafi muzgunawa da kuma kisan gillar da suka rika fuskanta a Rakhine.

Saida Khatun guda cikin ‘yan gudun hijirar wadda a gaban idonta sojin Myanmar suka yiwa mijinta ‘ya’yanta 3 da kuma mahaifanta kisan gilla, ta ce suna fatan yiwa shugabar gwamnatin ta Myanmar da manyan sojojin kasar hukunci mai tsanani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.