Pakistan

Kotu ta yanke wa tsohon shugaban kasa hukuncin kisa

Tsohon shugaban mulkin sojin Pakistan Pervez Musharraf.
Tsohon shugaban mulkin sojin Pakistan Pervez Musharraf. AFP Photos/Aamir Qureshi

Kotun Pakistan ta yanke wa tsohon shugaban mulkin sojin kasar, Pervez Musharraf hukuncin kisa bayan ta same shi da laifin cin amanar kasa. A karon farko kenan da ake yanke wa wani tsohon shugaban mulkin sojin kasar irin wannan hukuncin.

Talla

Kotun ta musamman da ke birnin Islamabad ta yanke hukuncin kisan ne a bayan idon Musharraf da ke gudun hijira, yayin da lauyansa ke cewa, an tuhume shi ne saboda matakinsa na jingine Kundin Tsarin Mulkin Pakistan tare da amfani da kudiri na musamman a shekarar 2007.

Matakin na wancan lokaci, ya haddasa zanga-zangar adawa da gwamnatin Musharraf, lamarin da ya tilasta masa murabus a daidai lokacin da aka fara zaman sauraren bahasin tsige shi daga karagar mulki.

Tun shekarar 2016 ne, Musharraf ya fice daga Pakistan da zummar neman magani a ketare bayan janye haramcin tafiye-tafiye da aka kakaba masa.

Tun daga wancan lokaci, Musharraf mai shekaru 76 ya fi yin balaguro tsakanin Dubai da birnin London.

Lauyan Musharaf ya ce, a halin yanzu, tsohon shugaban na fama da jinya a Dubai, yayin da ya kara da cewa, kawo yanzu, ba su tsayar da shawarar daukaka kara ba domin kalubalantar hukuncin kisan.

Musharraf wanda aka haifa a shekarar 1943 a birnin New Delhi na India, ya dare kan karagar mulkin Pakistan bayan kifar da gwamnatin Firaminista Nawaz Sharif a wani juyin mulkin da ba a zubar da jini ba a shekarar 1999.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI