India

'Manufar Modi ita ce mayar da India kasar Hindu zalla'

Firaministan India Narendra Modi
Firaministan India Narendra Modi REUTERS/Adnan Abidi

Zanga-zangar adawa da dokar hana Musulmai baki zama 'yan kasa a India ta tsananta, inda jama'a suka yi arangama da jami’an tsaro, yayin da masu sa ido a siyasar kasar ke kallon Firaminista Nerandra Modi a matsayin mai yunkurin mayar da kasar ta mabiya addinin Hindu zalla.

Talla

Zargin da akeyi wa Modi na shirin sauya alkibilar India ya soma ne bayan lashe zaben shugabancin kasar wa’adi na biyu a watan Mayu, inda a ranar 5 ga watan Agusta ya soke kwarya-kwaryar ‘yancin cin gashin kan Jammu da Kashmir, yanki daya tilo da Musulmi suka fi rinjaye a India, matakin farko kenan da masharhanta ke ganin ya jefa fargaba a zukatan al’ummar Musulmin kasar da adadinsu ya kai miliyan 200.

A watan Nuwamba kuma, kotun kolin India ta bai wa mabiya addinin Hindu damar gina katafaren wurin bautarsu a Ayodhya, wurin da a baya Musulmi suke da dadadden Masallacin da ya shafe shekaru sama da 400, nasarar da Jam’iyya mai mulki ta BJP ta dade tana fafutukar nema.

Wani batun da ya sake tabbatar da  zargin da ake yi wa Modi da shirin sauya alkibilar kasar, shi ne rajistar dan kasar da aka kammala a jihar Assam, inda aka ware akalla mutane miliyan 1 da dubu 900 akasrinsu Musulmi, wadanda a yanzu ke fuskantar barazanar rasa shaidar zama ‘yan kasa, tare da tsare su a wasu sansanoni da kuma korar wasunsu daga kasar baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI