Saudiyya da Pakistan sun kaurace wa taron kasashen Musulmin duniya

Musulmai daga sassa dabam - dabam na duniya na ibada a masallacin Ka'aba.
Musulmai daga sassa dabam - dabam na duniya na ibada a masallacin Ka'aba. REUTERS/Waleed Ali

Shugabanni da Wakilai daga Kasashen Musulmi na duniya 20 sun isa Kasar Malaysia domin gudanar da taron tattaunawa a kan matsalolin da suka shafi duniyar musulmi, taron da Saudiyya da Pakistan suka kaurace wa.

Talla

Ana sa ran wannan taro dake gudana a kaula lumpur ya lalubo hanyar magance dadaddiyar matsalar yankin Kashmir da kuma yankin Gabas ta tsakiya, da rikicin Syria da Yemen, da na musulmi yan kabilar Rohingya dake Myanmar, da tsanantar tayar da jijiyoyin wuya tsakanin alummar musulmi yan kabilar Uighur dake Yankin Xinjiang na Kasar China da kuma yadda za’a kawo karshen matsalar kyamar musulunci da musulmi a fadin duniya.

Shugaban Kasar Malaysia Mahathir Mohamad da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan sun gabatar da jawabi a taron wadda za’a shafe tsawon kwanaki 4 ana gudanarwa.

Shi kuwa Firaministan Pakistan Imran Khan, wanda tun farko da shi da takwarorinsa na Malaysia da Turkiyya suka tsara gudanar da taron, a karshe ya yanke hukuncin kauracewa taron.

A bayaninta na kaurace wa taron, Saudiyya ta bayyana cewa ba a wannan taro ne za’a tattauna matsalolin da suka shafi musulman duniya biliyan 1 da miliyan 750 ba, ko da yake masu sharhi na cewa kasar ta tsorata da fuskantar wariya daga kasashen Iran da Qatar da kuma Turkiya, wadanda shugabanninsu ke halartar taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI