India

'Yansandan India sun sake kashe musulmi masu zanga-zanga 5

Akalla mutane 5 aka tabbatar da mutuwarsu yau juma’a yayinda wasu da dama suka jikkata a wani sabon arangama tsakanin jami’an tsaron India da musulmin da ke zanga-zangar adawa da dokar hana mabiya addinin Islama shaidar zama ‘yan kasa.

Masu zanga-zanga a India.
Masu zanga-zanga a India. Reuters
Talla

Bayan sakkowa daga Sallar juma’a a babban masallacin kasar da ke jihar Uttar Pradesh ne dubun-dubatar musulmin suka fara zanga-zangar inda jami’an tsaro suka hallaka mutum biyar har lahira adadin da ya mayar da jumullar musulmin da jami’an tsaron na India suka kashe tun bayan fara zanga-zangar zuwa jumullar mutane 14.

Sabuwar dokar dai za ta saukakawa tsirarun addinai da ke gudun hijira a India daga kasashe 3 makokan kasar samun cikakkiyar shaidar zama ‘yan India amma banda mabiya addinin Islama, dokar da wasu ke kallo a wani yunkuri na Narendra Modi wajen ganin ya mayar da India ta mabiya addinin Hindu zalla.

Kisan na yau dai kari ne kan kisan wasu musulmai 3 da jami’an ‘yan sanda suka yi a jiya Alhamis lokacin da suka bude wuta kan masu zanga-zangar a arewa da kudanci biranen Lucknow da Mangalore.

Rahotanni sun bayyana cewa ilahirin mutanen da suka mutu harsashin ‘yansanda ne ya hallakasu yayinda wasu kuma tsabar duka ya yi sanadin rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI