Iraq

Masu zanga-zanga sun hana aikin hakar mai a Iraqi

Wani bangaren zanga-zangar kin jinin gwamnatin Iraqi, a babban birnin kasar Bagadaza.
Wani bangaren zanga-zangar kin jinin gwamnatin Iraqi, a babban birnin kasar Bagadaza. REUTERS/Thaier al-Sudani

Masu zanga-zanga a Iraqi, sun mamaye biranen kudancin kasar da dama, inda kuma suka tilasta dakatar da aikin hakar mai a filin Nassiriya inda ake hako gangar danyen mai dubu 82 a rana guda.

Talla

Karo na farko kenan da aikin hakar mai a Iraqi ya fuskanci kalubale, tun bayan barkewar zanga-zanga a sassan kasar.

Zanga-zangar kin jinin gwamnatin Adel Abdul Mahadi bisa zarginta da gazawa wajen samar da ayyukan yi gami da tabarbarewar tattalin arziki, na zuwa ne, a dai dai lokacin da jagororin siyasar kasar ta Iraqi ke fuskantar tsaiko a yunkurinsu na kokarin kafa sabuwar gwamnatin hadin gwiwa.

Yanzu haka dai Iraqi ce kasa ta biyu dake kan gaba wajen hakar danyen mai, a tsakanin kasashen dake da arzikinsa na kungiyar OPEC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.