EU ta bukaci gaggauta tsagaita wuta a Syria
Wallafawa ranar:
Kungiyar kasashen Turai EU, ta ce ya zama dole gwamnatin Syria da kawayenta su kawo karshen barin wutar da suke yi kan ‘yan tawaye, da wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda a lardin Idlib, abinda yayi sanadin halakar fararen hula da dama, da kuma tagayyara wasu dubbai.
Ministan harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turan Josep Borrell da ke wannan kira ya kuma dora alhakin hasarar rayukan daruruwan fararen hula a lardin kan gwamnatin Syria da Rasha.
A farkon watan Disambar nan kawancen dakarun Syria da Rasha suka kaddamar da sabon farmaki kan lardin na Idlib a arewacin kasar ta Syria, dake zama tungar karshe ta ‘yan tawayen kasar, duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin bangarorin a watan Agustan da ya gabata.
Wata kiddidiga da majalisar dinkin duniya ta fitar a baya bayan nan ta nuna cewar, a tsakanin 12 ga Disambar da muke zuwa 25 ga watan, luguden wutar dakarun na Syria da Rasha kan ‘yan tawaye, ya tilastawa fararen hula sama da dubu 2 da 35 tserewa daga muhallansu.
Wannan tasa a jiya lahadi kungiyar kasashen Turai ta bukaci kaiwa ‘yan gudun hijira akalla miliyan uku da har yanzu ke lardin na Idlib agajin gaggawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu