Taliban-Afghanistan

Taliban ta musanta shirin tsagaita wuta da gwamnatin Afghanistan

Wasu jagororin kungiyar Taliban.
Wasu jagororin kungiyar Taliban. AFP / KARIM JAAFAR

Kungiyar Taliban ta musanta jita-jitar tsagaita wuta tsakaninta da gwamnatin Afghanistan, jita-jitar da kafafen yada labaran kasar da na ketare yadawa wanda su ke ikirarin za ta kawo karshen yakin kasar na kusan shekaru 18.

Talla

Cikin sanarwar da Taliban ta fitar da safiyar yau litinin ta ce duk wani yunkurin tsagaita wuta ko kuma dakatar da yakinsu zai zo ne bayan ficewar dakarun Amurka daga kasar.

Taliban dai na ci gaba da tattaunawa da Amurka a yunkurin bangarorin biyu na kawo karshen yakin kasar da aka shafe kusan shekaru 18 ana yi, dai dai lokacin da a bangare bangaren Sojin na Taliban da Sojin gwamnatin Afghanistan ke ci gaba da yakar junansu bayanda Taliban ta ci gaba da tsananta kai farmaki.

Bangaren Amurka da gwamnatin Afghanistan sun jima suna neman gaggauta tsagaita wutar wadda kungiyar Taliban ta kalubalanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI