Amurka zata tura karin dakarunta sama da dubu 3 Gabas ta Tsakiya

Sojojin Amurka a Syria
Sojojin Amurka a Syria DELIL SOULEIMAN / AFP

Amurka ta ce za ta tura karin dakarunta dubu 3 da 500 zuwa yankin gabas tsakiya cikin shirin ko ta kwana, sa’o’i bayan halaka babban kwamandan dakarun juyin juya halin Iran na ketare da ta yi a gaf da filin jiragen saman birnin Bagadaza a Iraqi.

Talla

Matakin na Amurka da majiya mai tushe ta tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na AFP, na zuwa ne bayan da Iran ta sha alwashin mayar da zazzafan martani kan kisan babban kawamandan nata, a lokaci da kuma wurin da ya dace.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce sojin kasar sun halaka babban kwamandan dakarun juyin juya halin Iran a ketare Qassem Soleimani ne, saboda tabbacin da suke da shi cewar, kwamandan na kan shirye-shiryen kaddamar da munanan hare-hare kan muradun Amurka da sauran jami’anta a yankin gabas ta tsakiya.

Sai dai Pompeo yace Amurkan a shirye take, ta yi tattaunawar sulhu domin kaucewa barkewar yaki tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI