Iran ta nada sabon kwamandan dakarun ta a ketare

Janar Qassem Soleimani yayin wata ganawa da dakarun juyin juya halin kasar Iran
Janar Qassem Soleimani yayin wata ganawa da dakarun juyin juya halin kasar Iran AFP/Khamenei.IR/HO

Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamna’i ya bayyana Esma’il Qa'ani a matsayin sabon babban kwamandan dakarun juyin juya halin kasar a kasashen ketare, bayan da Amurka ta halaka tsohon kwamandan Qasem Solemani a Bagadaza

Talla

Da safiyar wannan Juma’ar ce dai wani jirgin yakin Amurka mara matuki yayi barin wuta kan tawagar motocin da kwamandan dakarun juyin juya hali na Iran a ketare Qasem Soleimani da wani takwaransa na Iraqi Abu Mahdi al-Muhandis ke ciki, yayinda suke shirin isa filin jiragen sama na Bagadaza da zummar tashi zuwa Iran.

Jim kadan da bayyanar labarin farmakin na Amurka ne, dubban jama’a suka gudanar da zanga-zangar A – Wadai da Amurka a birnin Teheran, yayinda jagoran addini na kasar ta Iran Ayatollahi al – Khamne’i ya sha alwashin mayarda da zazzafan martani kan ta’addancin da ya ce Amurkan ta yi musu na kashe Qasem Soleimani da ya kasance kusa wajen tasirin Iran a yankin gabas ta tsakiya.

Sai dai a bangaren Amurka tuni sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo ya ce a shirye suke ayi sulhu, yayinda ‘yan majalisun kasar suka ce ba’a sanar da su shirin kai farmakin ba, harin da kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta bayyana kashi Soleimani a matsayin gangancin da ka’iya haifar da mummunan sakamako.

Sai dai yayinda ake kokarin yayyafawa wutar dake neman tashi ruwa, shugaban Amurka Donald Trump yace tuntuni ya kamata ce an kawar da kwamdan na Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI