Japan-Lebanon

Ni kadai na tsara yadda na tsere daga Japan- Ghosn

Tsohon shugaban hadakar kamfanin Nissan da Renault Carlos Ghosn.
Tsohon shugaban hadakar kamfanin Nissan da Renault Carlos Ghosn. ERIC PIERMONT / AFP

Tsohon shugaban kamfanin kera motoci na Nissan Carlos Ghosn da a yanzu haka ya ke Lebanon, ya ce shi kadai ya tsara hanyar tserewa daga daurin talalar da ake masa a Japan ba tare da taimakon kowa ba.

Talla

Ghosn ya yi wannan ikirarin ne a dai dai lokacin da Turkiya ta tsare wasu mutane bakwai, ciki har da matukan jirgin sama 4, domin amsa tambayoyi kan yadda aka yi tsohon shugaban kamfanin na Nissan ya sauka a filin jiragen saman kasar da ke Istanbul, kafin karasawa Beirut babban birnin Lebanon.

Ranar litinin da ta gabata Carlos Ghosn ya tsere daga Japan bayan sulalewa jami’an tsaro ta barauniyar hanyar da kawo yanzu basu tantance ba, bayan da ya shafe sama da watanni 6 a karkashin dauri talala a gidansa.

A jiya Alhamis ne dai ma’aikatar shari’ar Lebanon ta bayyana samun umarni daga rundunar ‘yan sandan kasa da kasa ta Interpol, kan neman kame mata tsohon shugaban kamfanin kera motocin na Nissan Carlos Ghosn, wanda yake da tarkardar dan kasarda kuma Faransa.

Sai dai tuni gwmnatin Lebanon din ta ce babu wata yarjejeniya tsakaninta da Japan da za ta bada damar mika mata Ghosn, matsayarda itama Faransa ta dauka, inda tace ba za ta mikawa kowace kasa ko hukuma tsohon shugaban kamfannin na Nissan ba, muddin ya isa gare ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI