Raddin shugabannin duniya kan harin Iran a Iraki

Alamun makami mai Linzamin Iran tare da Jagoran juyin juya halin kasar Ayatollah Ali Khamenei
Alamun makami mai Linzamin Iran tare da Jagoran juyin juya halin kasar Ayatollah Ali Khamenei Nazanin Tabatabaee Yazdi/TIMA via REUTERS

Iran ta harba makamai masu linzami 22 kan sansanonin dakarun sojin hadin gwiwar da Amurka ke jagoranta a Iraqi.Yanzu haka dai bangarori daban daban na ci gaba da yin tsokaci kan farmakin, wanda shi ne na farko da Iran ta kaiwa Amurka, tun bayan kashe mata babban kwamanda Qasim Soleimani.

Talla

Cikin sanarwar da ta fitar a baya bayan nan, Majalisar Dinkin Duniya ta ce sam bai kamata a mayar da Iraqi dandalin gwabza yaki tsakanin Amurka da Iran ba, ganin yadda rikicin dake tsakaninsu ya dauki sabon salo.

Shi kuwa shugaban kasar ta Iraqi Barham Saleh, yayi Allah wadai da keta ‘yancin kasar ta hanyar maida ta fagen yaki, bayyana fargaba ya yi kan yadda yaki tsakanin Amurka da Iran, da ka iya yamutsa yankin gabas ta tsakiya saboda muninsa.

Yayin da yake nashi tsokacin kan zaman na dar dar a yankin Gabas ta tsakiya, Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, gargadin Iran yayi da cewar, za ta fuskanci kakkausan raddi muddin ta kai musu farmaki.

Sai dai yayinda masu gargadi, barazana, Allah–Wadai da kuma kokarin shiga tsakanin ke yi, wasu masharhanta na ganin, farmakin makamai masu linzamin har 22 da Iran ta kaiwa sojojin Amurka a Iraqi, tamkar gwajin ramuwar gayya ne, kan halaka mata babban kwamadanta Qasem Soleimani, akwai yiwuwar wasu jerin hare-haren a nan kusa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI