Asiya

Sarki Qabous na Oman ya rasu

Marigayi Sarki Qabous na Oman
Marigayi Sarki Qabous na Oman Mohammed Mahjoub / AFP

Allah ya yiwa Sarki Qabous na Oman rasuwa jiya juma’a, Sarki Qabous na Oman na daya daga cikin sarakunan da suka fi jimawa a karagar mulki, baya ga shafe kusan shekaru 50 ya na gadon sarrautar kasar ta Oman.

Talla

Sarki Qabous ya rasu ba tareda ya na da magaji ba, majalisar dake da nauyin tattance sabon sarki ta damkawa Ministan al’adu Haitham Bin Tariq dake dan uwa ga tsohon sarki mukamin sabon sarkin,wanda aka kuma rantsar da shi nan take a matsayin sabon sarkin Oman.

Marigayi Sarki Qabous, an dai haife shi a ranar 18 ga watan Nuwamba shekarar 1940 a Salalah dake yankin Dhofar a kudancin kasar, a shekara ta 1970 musaman ranar 23 ga watan Yuli ne ya hau gadon sarauta bayan wani juyin mulki da ya yiwa mahaifinsa a lokacin.

Hukumomin kasar sun ayyana zaman makoki na kwanaki 40.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.