China - Thailand

Sabuwar annobar murar mashako ta yadu daga China zuwa ketare

Wasu 'yan kasar China da suka rufe hancinsu saboda kaucewa kamuwa da kwayar cutar corona dake rukunin annobar murar mashako ta SARS.
Wasu 'yan kasar China da suka rufe hancinsu saboda kaucewa kamuwa da kwayar cutar corona dake rukunin annobar murar mashako ta SARS. AFP Photo/Noel Celis

Jami’an lafiyar majalisar dinkin duniya da na Thailand, sun tabbatar da cewa, wata sabuwar kwayar cuta, dake cikin rukuni guda annobar murar mashako ta SARS da ta tafka barna a shekarun baya, ta yadu zuwa wajen kasar China a karon farko.

Talla

An dai bankado bullar cutar murar mashakon ce dai a Thailand, bayan da likitocin kasar suka gudanar da gwaje-gwaje kan wani matafiyi dan kasar China da alamun cutar Pnuemomnia suka bayyana a tare da shi ranar 8 ga watan Janairun da muke ciki.

Bayan kammala binciken ne likitoci suka tabbatar da cewar mutumin ya kamu darashin lafiyar ce sakamakon harbuwa da kwayar cutar Corona dake cikin rukuni daya da annobar mashako ta SARS, wadanda suke haifarwa da mutum nuna alamun kamuwa da masassara mai alaka da sanyi, daga bisani kuma su yi karfin da zai kassara hanyoyin numfashin dan adam.

Tuni dai wannan kwayar cuta ta Corona ta harbi wasu mutane 41 da kuma kashe mutum guda a kasar China.

A tsakanin shekarun 2002 zuwa 2003 annobar cutar SARS ta halaka mutane 349 a China, sai kuma wasu karin mutanen 299 a yankin Hong Kong.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.