Cuta mai kamanceceniya da SARS ta fara yaduwa a Asiya

Kwayar cutar Sars-corona virus
Kwayar cutar Sars-corona virus Wikipédia

Annobar cutar da ke kamanceceniya da murar mashako ta SARS da ta bulla a baya-bayan nan a China ta hallaka mutum na 3 da ya kamu da ita, yayinda ake fargabar yaduwarta zuwa sauran sassan kasar da makota dai dai lokacin da al’ummar kasar ke shirin fara tafiye-tafiyen bukukuwan sabuwar shekarar China da ke tafe.

Talla

Mahukuntan kasar ta China sun yi gargadi kan yiwuwar yadawar cutar yayin bukuwan sabuwar shekarar yankin na Asia, bayan mutuwar mutum na 3 da cutar mai kamaceceniya da murar mashako ta SARS ta hallaka a yankin Wuhan.

Kawo yanzu dai kasashen Koriya ta kudu da Japan sun tabbatar da samun masu dauke da wannan cuta dake rukuni guda da murar Mashako ta SARS da aka samu bullarta a Chinan tun a ranar 8 ga watan nan na Janairu.

Mahukuntan na China dai sun nuna fargaba matuka la’akari da yadda birnin na Wuhan ke da yawan jama’a fiye da miliyan 11 baya ga kasancewarsa guda cikin manyan biranen zirga-zirga da ke yawan karbar baki daga ketare da ma sassan kasar.

Ko a shekarar 2002 zuwa 2003 cutar ta SARS ko kuma murar mashako sai da ta hallaka mutane 650 bayan samun barkewarta a Chinar da yankin Hong Kong.

Ma’aikatar lafiyar yankin Shanghai da ke tabbatar da yaduwar cutar a can, ta ce kawo yanzu mutane 218 aka tabbatar da sun kamu da ita, adadin da ke matsayin kari kan mutane 136 da suka kamu da ita a Wuhan baya ga wasu 15 a kudancin Guangdong da kuma wasu 5 a Beijing.

Tuni dai shugaba Xi Jinping na China ya tabbatar da daukar matakan gaggawa don yaki da cutar yayinda ya bukaci sanar da mahukunta da zarar an samu rahoton bullarta a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.