China

Cutar SARS na barazana ga kasuwancin China bayan kisan mutum 3

Yankin da aka killace wadanda suka kamu da cutar SARS mai kamanceceniya da murar mashako.
Yankin da aka killace wadanda suka kamu da cutar SARS mai kamanceceniya da murar mashako. REUTERS/Stringer CHINA OUT.

Hannayen jarin kasashen Asia sun fara sauka kasa bayan karuwar wadanda ke dauke da cutar nan ta SARS mai kamanceceniya da murar mashako a kasashen China da Hong Kong, inda kasuwanni suka gaza yin armashi yayinda kasashen biyu suka fuskanci faduwa a hada-hadar yau Talata.

Talla

A jiya Litinin ne, China ta nuna fargaba kan yadda Annobar cutar ta SARS mai kamanceceniya da murar mashako da ta bulla baya-bayan nan ta hallaka mutum na 3 da ya kamu da ita, inda kuma ta yadu zuwa kasashen Korea ta kudu da Japan dai dai lokacin da ake shirin fara tafiye-tafiyen bukukuwan sabuwar shekarar Nahiyar da ke tafe.

Kawo yanzu dai kasashen Korea ta kudu da Japan sun tabbatar da samun masu dauke da wannan cuta ta SARS dake rukuni guda da murar Mashako da aka samu bullarta a Chinan tun a ranar 8 ga watan nan na Janairu.

Mahukuntan na China dai sun nuna fargaba matuka la’akari da yadda birnin na Wuhan ke da yawan jama’a fiye da miliyan 11 baya ga kasancewarsa guda cikin manyan biranen zirga-zirga da ke yawan karbar baki daga ketare da ma sassan kasar.

Ko a shekarar 2002 zuwa 2003 cutar ta SARS ko kuma murar mashako sai da ta hallaka mutane 650 bayan samun barkewarta a Chinar da yankin Hong Kong.

Ma’aikatar lafiyar yankin Shanghai da ke tabbatar da yaduwar cutar a can, ta ce kawo yanzu mutane 218 aka tabbatar da sun kamu da ita, adadin da ke matsayin kari kan mutane 136 da suka kamu da ita a Wuhan baya ga wasu 15 a kudancin Guangdong da kuma wasu 5 a Beijing.

Tuni dai shugaba Xi Jinping na China ya tabbatar da daukar matakan gaggawa don yaki da cutar yayinda ya bukaci sanar da mahukunta da zarar an samu rahoton bullarta a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.