Asiya

China ta soke bukukwan sabuwar shekara

Likitoci masu kula da fasinjoji a China
Likitoci masu kula da fasinjoji a China Reuters

Hukumomi a China sun bayyana soke jerin bukukuwan sabuwar shekarar yankin Asiya da aka shirya a birane dabam-dabam, duk a cikin kokarin da kasar ke yi na dakile yaduwar cutar murar mashako wacce ake dangantawa da SARS, yayin da sauran kasashe ma ke daukar matakan kare kai daga wannan shu’umar cuta.

Talla

China ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen yin yekuwa ga al’umar ta cewa su kauce wa kutsawa wuraren da ake da cinkoson jama’a don hana yaduwar wannan cuta ta coronavirus,wacce tuni ta harbi mutane 570 birki.

Gwamnatin birnin Beijin ta bayyana aniyarta ta soke muhimman bukukuwa da ke jan hankalin dimbim masu yawon bude ido daga ko ina a fadin Duniya tsawon shekaru da dama, tana mai mika bukatar taimako daga al’ummarta.

Wadannan bukuwa da aka shafe shekaru da dama ana yi, na daga cikin manyan bukukuwan dake samun masu yawon bude ido daga cikin Chinan da ma wasu kasashen Duniya da suka kai milyan daya da dubu dari 4 cikin shekaru biyar da suka gabata.

Wannan cuta da ke kawo wa dan adam cikas wajen numfashi sai yaduwa take, inda a wannan Alhamis Vietanam ta bayyana gano mutane biyu da suka harbu da ita, yayin da Hong Kong ma ake fargabar cutar mashakon ta shake wasu.

A wani mataki na kare kai a Hadaddiyar Daular Laraba, hukumar filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Dubai, ta ce ba tare da bata lokaci ba za ta kaddamar da shirin yi wa fasinjojin da ke shigowa daga China gwaji don tanttace ko suna dauke da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.