Isa ga babban shafi
China

China ta dakatar da shige da fice a birane 4 saboda Corona

Wasu jami'an lafiyar China a garin Ruichang dake lardin Jiangxi. 25/01/2020.
Wasu jami'an lafiyar China a garin Ruichang dake lardin Jiangxi. 25/01/2020. ©cnsphoto via REUTERS.
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

China ta fadada matakin dakatar da zirga-zirgar shige da fice daga kan Beijing zuwa kan wasu karin manyan birnen da suka hada da Hubei, Shanghai da kuma Shandong, domin dakile ci gaba da yaduwar annobar murar mashako ta Corona.

Talla

Matakin killace biranen ya soma aiki ne a ranar lahadi, bayan da likitoci suka tabbatar da karuwar adadin wadanda annobar murar dake kassara hanyar numfashin bil adama ta kashe zuwa 56, yayinda kuma ta harbi wasu kusan dubu 2 a ciki da wajen kasar ta China.

Hukumomin birnin Wuhan na China, inda annobar murar mashakon ta corona ta soma bulla, sun ce adadin mutanen da suka kamu da cutar ya karu zuwa sama da dubu 1.

Yanzu haka dai Faransa, Amurka da kuma Japan sun yi shelar soma kwashe al’ummarsu daga kasar ta China.

A Faransa kuwa, magajiyar garin birnin Paris Anne Hidalgo ce tasanar da soke bikin faretin sabuwar shekara da aka saba yi a birnin, domin tsaurara matakan dakile yaduwar annobar murar da corona, da ta bulla a kasar ranar Juma’ar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.