Taliban-Amurka

Taliban ta yi ikirarin kakkabo jirgin Amurka a Afghanistan

Mayakan kungiyar Taliban.
Mayakan kungiyar Taliban. Parwiz/REUTERS

Kungiyar Taliban ta yi ikirarin kakkabo jirgin Sojin Amurka da ya fado jiya Litinin a yankin gabashin Afghanistan, yankin da ke da rinjayen mayakan kungiyar.

Talla

Sa’o’I kaliban bayan fadowar jirgin na sojin Amurka jiya Litinin, kungiyar ta Taliban ta fitar da sanarwa tare da ikirarin cewa ita ke da alhakin kakkabo jirgin wanda ya hallaka ilahirin mutanen da ke cikinsa.

Sanarwar tare da ikirarin na Taliban na zuwa ne bayan da gwamnatin Afghanistan ta musanta hadarin wanda ta ce babu ko da guda cikin jiragenta na yaki ko na Fasinja da ya yi hadari, yayinda kungiyar tsaro ta NATO ta gaza cewa komi game da harin.

Zabihullah Mujahid shi ne kakakin kungiyar Taliban, cikin sanarwar da ya fitar a yaruka 3, ya ce mayakansu ne suka kakkabo jirgin ko da dai sanarwowin sun ci karo da juna inda wata ta daban ta nuna cewa jirgin da kansa ya fado a yankin Ghazni da ke karkashin ikon Taliban.

Yankin na Ghazni da ke karkashin ikon mayakan na Taliban na matsayin yaki mafi hadari ga jami’an tsaron gwamnati ko kuma hadakar Sojin NATO da ke yaki a Afghanistan.

Sai dai Rohullah Ahmadzai kakakin ma’aikatar tsaron Afghanistan ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa, jirgin da mayakan ke ikirarin kakkabowa ba mallakin Sojin kasar ko kuma ma’aikatar leken asirinta ba ne.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan yawan jami’an da ke cikin jirgin wanda da farko aka bayyana da kamfanin Ariana mallakin kaar kafin daga bisani Taliban ta bayyana shi dana Sojin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.