China-Corona

Cutar Corona: Dubu 14 sun harbu, 300 sun mutu

Wani mai binciken cutar coronavirus a wata cibiya a Paris
Wani mai binciken cutar coronavirus a wata cibiya a Paris Thomas SAMSON / AFP

Kasar Philippines ta sanar da asara rai ta farko a wajen China sakamakon sabuwar cutar Corona virus, lamarin da ya ta’azzara  faragaba a zukatan kasashen duniya game da annobar da ya zuwa yanzu ta lakume fiye da rayuka 300.

Talla

Munanar wannan cuta ta farko a wajen kasar China na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatocin kasashen duniya suka garkame iyakokinsu ga masu shigowa daga China, inda cutar ta samo asali a kokarinsu na dakile yaduwarta.

Tun da wannan cuta ta bulla a birnin Wuhan dake tsakiyar China a karshen shekarar da ta gabata, ta harbi mutane sama da dubu 14 a fadin kasar, kana ta yadu zuwa wasu kasashe 24.

Kasashen duniya dai na ta daukan matakan kare kai daga wannan cuta, inda a kusan karshen makon nan Rasha ta rufe iyakarta da China daga gabashin kasar, yayin da kasar Kazakhstan ta hana motocin bus bus da jiragen kasa ketarowa zuwa kasarta daga Chinan.

Mongolia ta garkame iyakarta ga motoci masu shigowa, yayin da Koriya ta Kudu, wacce saniyar ware ce, dake dogaro da alakarta da China, ta haramta wa masu yawon bude ido shigowa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.