OIC ta yi watsi da shirin Trump na sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya

Hoton mambobin kungiyar kasashen muslmai ta OIC
Hoton mambobin kungiyar kasashen muslmai ta OIC Reuters

Kunigiyar Musulmi ta Duniya OIC ta yi watsi da shirin Shubagabn Amurka Donald Trump na tsasanta rikicin gabas ta tsakiya, inda tayi kira ga daukacin membobin ta 57 da kada su baiwa shirin goyon baya.

Talla

Kungiyar dake wakiltar musulmi biliyon 1.5 a duk fadin duniya taki amin cewa da shirin da bai wakilci dukanin bangarori ba da kuma hakkin Falastinawa.

A wani taro na ministocin harkokin waje da ya gudana a shelkwatar kungiyar dake birin Jidda a Saudiya sun bukaci duk mambobin su suki amin cewa da matakin gomnatin Amurka na tilastawa akan wannan shirin, da tuni ya mallakawa Isra'ila Birnin Kudus amatsayin babban birninta.

Kungiyar ta jaddada goyaon bayan ta ga kasancewar gabashin birnin kudus a matsayin babban birnin Falasdinawa.

Tace zaman lafiya zata inganta ne kawai idan isara’ila ta janye daga kawanyan da tayiwa yankunan Falasdinawa a karshen yakin gasaba ta tsakiya a shekara 1967.

Itama kungiyar larabawa tayi Allah wadai da wannan shirin na Donald Trump a wani taron data gudanar a birin Kairon Masar, inda tace wannan shirin bai samar da matsayi ba ga al'ummar Falasdinu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.