WHO-Corona

WHO ta kaddamar da gidauniyar yakar annobar cutar Coronavirus

Matakan yaki da cutar Corona a China.
Matakan yaki da cutar Corona a China. photo via REUTERS. ATTENTION EDITORS

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ta kaddamar da gidauniyar Dala miliyan 675 domin tinkarar cutar coronavirus da ke cigaba da hallaka jama’a musamman a kasar China da sauran kasashen yankin Asia da ta bazu.

Talla

Shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Gebreyesus ya sanar da gidauniyar a Geneva wadda ya ce za’ayi amfani da ita a cikin watanni 3 masu zuwa.

Jami’in ya ce hukumar za ta kashe Dala miliyan 40 wajen aikin ta, yayin da sauran kudin za’a taimakawa kasashen da cutar ta shafa.

Tuni Gidauniyar Bill da Milinda Gates suka sanar da bayar da tallafin Dala miliyan 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.