Isa ga babban shafi
Amurka-Taliban

Amurka ta kulla kwarya-kwaryar yarjejeniyar zaman lafiya da Taliban

Wakilcin jagorancin kungiyar Taliban yayin tattaunawar farko kan shirin sasanta rikicin kasar.
Wakilcin jagorancin kungiyar Taliban yayin tattaunawar farko kan shirin sasanta rikicin kasar. AFP / KARIM JAAFAR

Kasar Amurka ta gabatar da kunshin kwarya-kwaryar yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kulla da kungiyar Taliban a Afghanistan, yarjejeniyar da ake fatan ta takaita tashe tashen hankula da musayar wuta daga bangarorin biyu na tsawon mako guda a fadin kasar.

Talla

Wani jami’in gwamnatin Amurka ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, takaita tashin hankalin nada matukar muhimmanci, kuma ya shafi bangarori da dama har da na gwamnatin Afghansitan.

Rundunar sojin Amurka wadda ke da jami’ai tsakanin 12,000 zuwa 13,000 a cikin Afghansitan za su sanya ido kan abubuwan da ke faruwa domin tabbatar da cewar mayakan Taliban na aiwatar da yarjejeniyar.

Jami’in ya ce Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya tattauna kan cigaban da aka samu tare da shugaba Ashraf Ghani a taron tsaron da ke gudana a birnin Munich na kasar Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.