Syria-Damascus

Zirga-zirgar jiragen sama ta dawo gadan-gadan a Syria bayan shekaru 8

Shugaba Bashar al-Assad na Syria.
Shugaba Bashar al-Assad na Syria. REUTERS/SANA/Handout via Reuters

A karon farko cikin shekaru 8 Jirgin fasinja ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Aleppo a kasar Syria mai fama da yakin basasa tsawon shekaru.

Talla

Matakin dawo da zirga-zirgar jiragen saman a Syria na zuwa bayan da gwamnati ta bayar da sanarwar kwace manyan birane 2 ciki har da Aleppo daga hannun ‘yan tawayen kasar.

A karon farko gwamnati ta Syria karkashin Bashar al- Assad bisa taimakon Sojin kawance na Rasha ta kuma bude manyan hanyoyin da suka sada sassan kasar hudu wadanda suka kasance a rufe tun cikin shekarar 2012.

Tun a jiya Talata ne gwamnatin Syria ta sanar da cewa za a dawo da zirga-zirgar jiragen saman daga yau Laraba matakin da ke matsayin babban ci gaba ga bangaren sufuri da tattalin arzikin kasar.

Yanzu haka dai jirage za su rika tashi daga biranen Aleppo da Damascus zuwa sauran sassan kasar da makwabta ciki har da Masar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.