Taliban-Afghanistan

Shugaban Afghanistan ya yi watsi da bukatar sakin 'yan ta'adda 5000

A Lahadin nan shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya ce kwarya kwarya yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanan bakwai da aka cimma da Taliban ta na nan daram, sai dai ya yi watsi da bangaren yarjejeniyar da ke kira da ya saki dubban ‘yan ta’adda da ke gidajen yarin kasar.

Ashraf Ghani, shugaban kasar Afghanistan.
Ashraf Ghani, shugaban kasar Afghanistan. REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

An yi kwananki bakwai ba tare da kai hare hare ba tsakanin bangrorin dake kai ruwa rana a kasar, gabanin yarjejeniyar da aka cimma ranar Asabar tsakanin Talibn da Amurka a Doha.

Bisa ga yarjejeniyar, a cikin watanni 14 sojojin kaashen waje za su bar kasar, amma fa da sharadin Taliban za ta cika alkawuran da ta dauka, ciki har da tattaunawa da gwamnatin Afghanistan kan zaman lafiya mai dorewa.

Bayan kusan shekaru 20 na yaki da ya daidaita Afghanistan tare da jefa al’ummarta cikin matsanancin yunwa, Amurka da Taliban a jiya Asabar sun sanya hannu a wata yarjejeniyar da Amurka ke fata zata kawo karshen yakin da ta fi kwashe tsawon lokaci tana yi.

Yarjejeniyar da aka cimma a birnin Doha na kasar Qatar za ta kai Amurka da aminanta na kasashen waje ga janye dakarun su a Afghanistan a cikin watanni 14,amma da sharadin Taliban za ta cika alkawarin da ta yin a hawa teburin tattaunawa gwamnatin Afghanistan da ke samun goyon bayan kasashen yammacin Turai, kana tayi silar ficewa masu ikirarin jihadi a kasar, ciki har da Al-Qaeda.

A shekarar 1996 ne dai kungiyar Taliban ta karbe mulkin kasar Afghanistan, inda daga nan ne ta fara tafiyar da kasar bisa tsarin shari’ar Musulunci, har ma ya kai ga haramta wa mata yin aiki, tare da rufe makarantun mata da kuma haramta kade kade da duk wani al’amari na nishadi.

Tun bayan mamayar kasar ta Afghanistan karkashin jagorancin Amurka, biyo bayan harin ta’addanci da aka kai biranen New York da Washington a shekarar 2001, Amurkan ta kashe sama da dala tiriliyan daya wajen yaki da sake gina kasar.

Kimanin sojojin Amurka 2,400 ne suka mutu a yakin, tare da dubban sojojin Afghanistan da dakarun Taliban.

Duk da kyautata zato da ake, yarjejeniyar ta Doha ta saka fargaba a zukatan wasu ‘yan Afghanistan, inda suke ganin suna iya rasa kwarya kwarya rayuwa ta yanci da suke yi a halin yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI