Turkiya-Syria

Turkiya ta kaddamar da farmaki kan sojin Syria

Wasu  tankokin yakin Turkiya a gaf da shiga lardin Idlib dake arewacin Syria.
Wasu tankokin yakin Turkiya a gaf da shiga lardin Idlib dake arewacin Syria. REUTERS/Khalil Ashawi

Turkiya ta tabbatar da kaddamar da farmaki kan dakarun gwamnatin Syria da ke samun goyon bayan Rasha.

Talla

Turkiyar ta kuma matsa lamba kan Turai ta hanyar bude kan iyakokinta domin bai wa ‘yan gudun hijira damar kwarara cikin nahiyar.

Tankiya ta tsananta tsakanin Rasha da Turkiya bayan wani farmakin jiragen sama da aka zargi gwamnatin Syria da kaddamarwa, harin da ya kashe sojojin Turkiya akalla 33 a lardin Idlib cikin makon jiya.

Sojojin Turkiya da na Syria sun yi musayar wuta a tsakaninsu a karshen mako, inda dakarun na Syria suka yi ta yunkurin kakkabo jirgi mara matuki na Turkiya wadda ita kuma ta yi ikirarin harbo jiragen yakin Syria guda biyu. Zalika Turkiyan ta bayyana samun nasarar halaka sojojin Syria 16, yayin farmakin data kai musu har kashi 200.

Lamurra dai na gab da rincabewa baki daya a yankin Idlib da ke karkashin ikon ‘yan tawaye, lura da yadda dakarun Syria suka kara kaimin hare-hare tare da kashe daruruwan fararen hula a yunkurinsu na sake karbe tungar karshen ‘yan tawayen.

Yanzu haka dai, fito-na-fiton da aka samu tsakanin dakarun Syria da na kasar Turkiya wadda ke zama mamba a kungiyar tsaro ta NATO, ya haifar da damuwa, lura da yadda rikicin ka iya fadada da kuma haddasa karin kwararar ‘yan gudun hijira zuwa Turai irin yadda aka gani a shekarar 2015.

Tuni dai shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya sanar da bude kofa ga ‘yan gudun hijira domin fantsama cikin Turkiya ta hanyar Girka.

Ko a jiya Lahadi sai dai kasar ta Girka ta ce, ta dakile kusan ‘yan gudun hijira dubu 10 akan iyakarta da Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI