Coronavirus ta kashe mutane 287 a kwanaki 2

Wani dan yaro sanye da kariyar kamuwa da cutar coronavirus
Wani dan yaro sanye da kariyar kamuwa da cutar coronavirus REUTERS/Remo Casilli

Cutar Coronavirus dake cigaba da hallaka rayuka a kasashen duniya yanzu haka ta shiga kasashe 107, inda ta kama mutane 117,339, yayin da ta hallaka 4,251.

Talla

Wannan ya nuna cewar daga Litinin zuwa Laraba an samu karuwar sabbin mutane 4,084 da suka kamu da cutar, yayin da 287 suka mutu.

A kasar China kawai inda cutar tafi illa, banda yankunan ta na Hong Kong da Macau, mutane 80,754 suka kamu da ita, yayin da 3,136 suka mutu, kuma bincike ya nuna cewar 59,897 sun warke.

A wajen China kasar Italia ke gaba wajen samun mutane 10,149 da suka kamu da cutar, kuma 631 sun mutu, sai Iran mai dauke da mutane 8,042 da suka kamu, kuma 291 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.