Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta sake gwajin sabbin makamai

Korea ta Arewa ta yi gwajin sabbin makamai masu linzami guda 2 masu cin gajeren zango, wadanda ta harba a gabar ruwanta zuwa cikin teku.

Korea ta Arewa tayi gwajin makamai masu linzami.
Korea ta Arewa tayi gwajin makamai masu linzami. REUTERS
Talla

Yayin tabbatar da gwajin makaman, rundunar sojin Korea ta Kudu ta yi Allah-wadai da gwajin makaman, wanda tace bai dace ba, la’akari da yanayin da duniya ke ciki na fafutukar tsira daga kaifin annobar murar Coronavirus.

Har yanzu dai Korea ta Kudu bata bada rahoton bullar annobar cikin kasar ba, cutar da kawo yanzu ta halaka rayuka sama da dubu 11, gami da shafar wasu sama da dubu 270 bayan kutsawa cikin kasashen da manyan yankuna 157.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI