Kwana ta 3 a jere babu wanda coronavirus ta kama a China
Duk da karuwar masu kamuwa da cutar coronavirus a sassan duniya, an shiga kwana ta uku a jere a Asabar din nan da ba a samu rahoton sabbin kamuwa da cutar ba.
Wallafawa ranar:
A makonnin da suka wuce, an yi ta samun raguwar masu harbuwa da cutar a China yayin da sauran sassan duniya suka kara azama wajen daukar matakan yaki da annobar.
A ranar Juma’a hukumar lafiya ta duniya ta jinjina wa China da nasarar da ta samu wajen cin karfin wannan cuta a tsakiyar birnin Wuhan, inda aka fara samun bullar cutar a karshen shekarar da ta gabata.
Kimanin mutane miliyan 56 ne aka killace a birnin Wuhan da kewayen lardin Hubei a karshen watan Janairu, amma a sannu a hankali hukumomin yankin suna sassautawa a game da batun takaita zirga zirga duba da saukin da ake samu wajen yawan masu kamuwa da cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu