China za ta baiwa al'ummar lardin Hubei damar fara shige da fice
Mahukunta a China sun ce za a bai wa jama’a damar yin shige da fice a a lardin Hubei inda kwayar cutar Coronavirus ta samo asali, bayan share tsawon watanni biyu cur jama’a sama da milyan 50 na kulle a gidajensu.
Wallafawa ranar:
Matakin wanda zai fara aiki ranar 8 ga watan gobe, zai bai jama’a damar fita don gudanar da wasu lamurran yau da kullum tare da ziyartar ‘yan uwa, inda filayen sauka da tashin jiragen sama guda uku da ke yankin za su fara jigilar fasinja.
Sai dai cikin matakan na mahukuntan China har yanzu baza a sahalewa makarantun yankin budewa ba, batun da ke nuna cewa miliyoyin dalibai za su ci gaba da kasancewa a gida.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu