China ta sanya dokar hana baki shiga sassanta har 'yan asalin kasar
Hukumomi a China sun hana ‘yan kasashen waje shiga kasar, yayin da kuma suka kudiri aniyar hana wadanda ke da biza da izinin zaman kasar izinin shiga kasar duk dai a wani mataki na dakile yiwuwar sake samun ta’azzarar cutar a kasar.
Wallafawa ranar:
Sauran matakan da aka dauka sun hada da rage yawan jiragen da ke tashi zuwa kasashen waje, da kuma rage yawan fasinjoji da jiragen ke kwashewa da kashi 75.
A ‘yan makonnin da suka wuce, yawan masu kamuwa da cutar coronavirus ya ragu a China, amma matsalar ta sake kunno kai bayan wasu da suka kamu da cutar sun isa kasar daga kasashen waje.
Kawo yanzu dai cutar ta corona ko kuma COVID-19 da ta samo asali daga China ta fantsama zuwa kasashe 182 inda ta hallaka mutane fiye da dubu 26 galibinsu a nahiyar Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu