Coronavirus-China

Lamurra sun soma daidaita a birnin Wuhan bayan shafe watanni a killace

A karon farko bayan shafe awatanni biyu a killace babu shiga babu fita, harkokin yau da kullum sun soma daidaita a birnin Wuhan dake China, inda annobar coronavirus ta soma bulla.

Wasu daga cikin dubban fasinjojin farko da suka isa birnin Wuhan makyankyasar annobar coronavirus, bayan soma daidaitar lamurra a birnin dake lardin Hubei. 28/3/2020.
Wasu daga cikin dubban fasinjojin farko da suka isa birnin Wuhan makyankyasar annobar coronavirus, bayan soma daidaitar lamurra a birnin dake lardin Hubei. 28/3/2020. REUTERS/Aly Song
Talla

Yanzu haka dai dubban fasinjoji ne suka shiga birnin na Wuhan a jirgin kasa, bayan soma aikin tashohin layin dogon da annobar murar ta tilasta dakatarwa a watannin baya.

A makon gobe ne kuma ake sa ran bude manyan shagunan saida kayayyaki a birnin na Wuhan.

A halin da ake ciki annobar coronavirus ta halaka jimillar mutane dubu 3 da 295 a kasar China bayan bulla a birnin Wuhan cikin watan disamban 2019.

Daga cikin akalla dubu 82 da suka kamu da cutar a kasar ta China kuma, kusan dubu 70 sun samu waraka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI