Dubban 'yan Lebanon na zanga-zanga kan durkushewar tattalin arziki

Daya daga cikin masu zanga-zanga a birnin Bierut na kasar Lebanon, yayin jifa da kwanson hayaki mai sa hawaye.
Daya daga cikin masu zanga-zanga a birnin Bierut na kasar Lebanon, yayin jifa da kwanson hayaki mai sa hawaye. AFP

Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga zanga a kasar Lebanon saboda tabarbarewar tattalin arziki, abinda ya haifar da arangama tsakanin su da jami’an tsaro duk da killace mutane da aka yi a gidajensu.

Talla

Rahotanni sun ce maza da mata da kananan yara sun shiga zanga-zangar akan titunan Tripoli, birni mafi girma a kasar, inda masu zanga-zangar suke wakar neman juyin-juya hali.

Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye, yayin da sojoji suka yi harbi sama lokacin da masu zanga-zangar suka yi kokarin shiga majalisar dokoki, yayinda wasu suka yi ta cinna wuta a bankuna.

Kasar Lebanon na fuskantar durkushewar tattalin arziki mafi muni a tarihinta, tun bayan wanda ta fada ciki a tsakanin shekarun 1975 zuwa 1990, lokacin da yakin basasa ya barke a kasar.

Masu sharhi kan lamurran yau da kullum dai sun alakanta tagayyarar tattalin arzikin Lebanon da matakin kafa dokar hana fitar da gwamnati tayi, da kuma rufe ilahin masana’antu, da hukumomin dake kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.