India

Mutane 9 sun mutu, dubu sun jikkata dalilin shakar iska mai guba

Masu aikin ceto yayin kwashe mutanen da suka shaki iskar gas mai guba daga kamfanin LG Polymers a Visakhapatnam, dake jihar Andhra Pradesh.
Masu aikin ceto yayin kwashe mutanen da suka shaki iskar gas mai guba daga kamfanin LG Polymers a Visakhapatnam, dake jihar Andhra Pradesh. AFP

Akalla mutane 9 suka mutu, yayinda aka ruga da akalla wasu dubu 1 ko sama da haka zuwa asibiti, sakamakon shakar iskar gas daga wani kamfani mai suna LG Polymers dake India.

Talla

Swaroop Visakhapatnam, jami’ar Yan Sanda ta tabbatar da mutuwar mutanen 5, da kuma kwantar da akalla 70, yayin da ake duba lafiyar wasu tsakanin 200 zuwa 500.

Jami’ar tace wani tanki mai dauke da iskar gas akalla ton dubu 5,000 ne yayi ta tsiyaya ba’a sani ba, saboda killace mutane a gida sakamakon yakin da cutar coronavirus.

Hotunan bidiyon dake yawo a kafafen sadrwa na zamani, sun nun mata da kananan yara kwance a kasa cikin mawuyacin hali, bayan shaker gubar ta gas a titunan unguwar Visakhapatnam dake jihar Andhra Pradesh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI