Saudiya

Saudiya ta rubanya haraji sau 3 kan kayayyakin da ake kaiwa cikinta

Saudiya ta soma aiwatar da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati, don sake karfafa tattalin arzikinta.
Saudiya ta soma aiwatar da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati, don sake karfafa tattalin arzikinta. AFP/File / FAYEZ NURELDINE

Gwamnatin Saudi Arabia ta sanar da rubanya harajin kayayyakin kasashen ketare da ake sayarwa a kasar da ake kira VAT har sau 3.

Talla

Saudiyan ta kuma katse kudaden tallafin da take baiwa jama’ar kasar a sabon shirinta tsuke bakin aljihun da ta gabatar a yau, sakamakon cigaba da faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya.

Kafafen yada labaran Saudiya sun ce, wannan matakin da gwamnati ta dauka zai taimaka wajen bunkasa asusun ajiyar kasar da kimanin Riyal biliyan 100, kwatankwwacin dala biliyan 26.6, kuma hakan na zuwa ne a daidai lokacin da mahukunta suka kara kaimi wajen rage kashe kudade domin farfado da tattalin arzikin kasar.

Sai dai ana ganin al’ummar kasar za su nuna adawa da shirin na tsuke bakin aljihun gwamnati, lura da cewa, sun dade suna fama da matsalar tsadar rayuwa kafin sanar da sabon shirin.

Zalika, ana ganin ‘yan kasar za su kara kaimi wajen sanya ido kan wasu ayyukan biliyoyin kudade da gwanmnatin kasar ke gudanarwa, da suka hada da shirinta na sayen Kungiyar Kwallon Kafa ta Newcastle da ke Ingila.

Ministan Kudin Saudiya Mohammed al-Jadaan, ya ce daga watan Yuni mai zuwa, gwamnatin za ta daina baiwa ‘yan kasar kudeden alawus-alawus, sannan kuma za a rubanya harajin kayayyaki daga kashi 5 zuwa kashi 15 daga ranar 1 ga watan Yuli.

A kokarin sanyaya zukatan ‘yan kasar biyo bayan daukar matakin na tsuke bakin aljihu, Babban Kamfanin Makamashi na Kasar ta Saudiya wato Aramco, ya zaftare farashin mai a cikin gida da kusan rabi a yau Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.